Daga Hafsat Lawan Sheka
Shugaban kungiyar likitocin Najeriya NMA, ya yi kira ga mambobin kungiyar da su kwantar da hankalinsu, kuma wadanda ke aiki a asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake Kano su koma bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.
Hakan ya biyo bayan ganawar da sukai da shugaban asibitin, da babban sakataren hukumar kula da asibitocin Kano, kwamishinan lafiya, da kwamishinan ‘yan sanda, dangane da lamarin da ya faru a sashin masu haihuwa na asibitin.
Tun da farko, likitoci, ma’aikatan jinya, da sauran ma’aikata a asibitin sun kauracewa ayyukansu a asibitin don nuna adawa da harin da aka kaiwa wani abokin aikinsu.
APC da Yahaya Bello Sun Magantu Kan Neman Kujerar Ganduje
Rahotanni sun nuna cewa dangin wata mata mai juna biyu da ta mutu a lokacin tiyata ne, suka kai wa likitan da ke bakin aiki, inda suka yi garkuwa da shi na tsawon sa’o’i.
Marasa lafiya da suka ziyarci asibitin sun kasance cikin wani mawuyacin hali yayin da likitoci, ma’aikatan jinya, da sauran ma’aikata ba sa nan saboda fargaba.
Shugaban kungiyar likitocin Najeriya NMA reshen jihar Kano Dr. Sulaiman Abdullahi yayi karin haske inda ya bukaci gwamnatin jihar, ma’aikatar lafiya ta Kano, da hukumar kula da asibitocin jihar Kano (HMB), da jami’an tsaro, da duk masu ruwa da tsaki da su tabbatar da sun yi duk mai yiwuwa don kare lafiyar likitoci da sauran ma’aikatan jinya a asibitin.
Sabon Gwamnan Kogi Ya Zo da Sabon Salo a Dimokaradiyyar Nigeria
Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano (HMB), Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan harin da wasu suka kai wa wani likita a asibitin. Ya kuma bai wa likitocin da kungiyar su tabbacin tsaron lafiyarsu tare da yin kira ga hukumar da ta baiwa mambobinsu damar ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum a asibitin.
“Daraktocin hukumar, da hukumomin tsaro daga rundunar ‘yan sanda da DSS, da wakilan NMA, SSD, NGDP suka yi taron gaggawar, kuma an dauki matakan da suka dace. Wani bangare na matakin da aka dauka shi ne gurfanar da wadanda suka aikata laifin, domin za a dauki matakin shari’a kan duk wanda aka samu da laifi.
Har ila yau, za a karawa jami’an tsaron asibitin kaimi, da kuma kara yawansu a kofofin shiga da fita, da jami’an tsaro a wuraren da suka fi daukar hankali a cikin asibitin, da kuma kara wayar da kan jama’a kan yadda za a shawo kan matsalolin asibitoci.”