Kudirin mu na Samar da Gidaje a Nigeria Gaskiya ne – Minista T Gwarzo

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane na Nigeria Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya bayyana cewa ma’aikatar na kokarin ganin an tabbatar da shirin “Renew Hope Agenda” wato Sabunta Fatan Nigeria na shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu kan aikin samar da gidaje a Kasar.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar likitoci da likitan hakora da suka kai masa ziyarar ban girma a ofishin sa.

Ministan ya bayyana cewa kungiyar ta kasance mai matukar muhimmaci kuma abokiyar tarayya wajen samar da gidaje masu inganci da lafiya a Nigeria .

APC da Yahaya Bello Sun Magantu Kan Neman Kujerar Ganduje

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga Ministan kan harkokin yada labarai Adamu Abdullahi, ya aikowa kadaura24.

Ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba, Shugaba Bola Ahmad Tinubu zai kaddamar da aikin gina “Mega City project” a karkashin shirin “Renew Hope Agenda” na samar da gidaje masu saukin kudi ga daukacin ‘yan Najeriya.

Sabon Gwamnan Kogi Ya Zo da Sabon Salo a Dimokaradiyyar Nigeria

Ministan ya yabawa kungiyar bisa hangen nesa na neman hadin kan ma’aikatar tare da ba da tabbacin yin aiki tare da su wajen samar da gidaje masu inganci a fadin kasar nan.

Tun da farko shugaban kungiyar na kasa Farfesa Muhammad Aminu Muhammad ya shaida wa Ministan cewa sun je ofishin sa ne domin su sadu da shi a kan ayyukan kungiyar da kuma neman hadin kai ta fannin samar da gidaje masu sauki, aminci da kwanciyar hankali bisa ga doka tare da tsarin kiwon lafiya.

Farfesa Muhammad wanda ya bayyana ayyukan kungiyar da suka hada da horar da daliban likitanci da ke da sha’awar zama masu ba da shawara, ya bukaci ministan da ya saukaka rabon fili a Abuja domin kungiyar ta gina babban ofishinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...

Zargin kisa a R/Zakara: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamiti – Waiya

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da...

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...