Wata kididdiga da kungiyar Transparency International ta fitar kan rashawa ta nuna cewa an samu ci gaba wajen yaki da matsalar a Najeriya inda a yanzu kasar ke mataki na 145 cikin kasashe 180 da aka yi nazari a kai.
Kididdigar ta nuna cewa Najeriya ta kara maki daya kan maki 24 da take da shi a baya inda a yanzu take da maki 25 cikin 100 baya ga matsawa daga matsayinta na 150.
Kotun Ƙoli: Shin da gaske ne an kwalla yarjejeniya tsakanin Gwamnan Kano da Tinubu ?
Kididdigar na duba yadda yanayin matsalar rashawa take a gwamnatin kasashen da aka yi nazari akan su.
Tana bai wa kowace kasa maki daga 0 zuwa 100 – 0 na nufin matsalar rashawa ta yi katutu yayin da 100 ke nufin nasara a yaki da rashawa.
Sabon Gwamnan Kogi Ya Zo da Sabon Salo a Dimokaradiyyar Nigeria
Cibiyar Rajin Kyautata Ayyukan Majalisun Dokoki da Yaƙi da Rashawa a Najeriya CISLAC wadda ta gabatar da jadawalin a Abuja, ta ce makin da Najeriya ta samu kasa yake da maki 33 na kasashen da ke kudu da hamadar sahara.
Jadawalin bai fito da bayanan rashawa ba a kasar amma ya bayyana yadda ake kallon cin hanci a Najeriya.
Cislac ta ce kididdigar ba wai tana nazarin ayyukan hukumomin yaki da rashawa ba ne da ta ce suna kokari wajen yakar cin hanci a Najeriya.