Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kwanaki kadan bayan fitar rahoton jaridar kadaura24, gwamnatin jahar Kano, karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf , ta dakatar da shugaban gidan Rediyon jihar Kano Hisham Habib, nan ta ke tare da umartar mataimakin shugaban tashar Abubakar Adamu Rano, da ya cigaba da jagorantar tashar Rediyon.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito ana zargin Hishan Habib da cefanar da wata mota ta yada shirye-shirye daga waje wato OB Van sai injin bada hasken wutar lantarki wato Janareto da tankin ajiye ruwa wato overhead tank.

Sanarwar dakatarwar na dauke a cikin wata takadda da mukaddashin sakataren gwamnatin jahar Kano Abdullahi Musa ya sanyawa hannu a ranar juma’a.
Gidan Radeyon gwamnatin jahar Kano ya na dauke da tashoshi guda biyu da suka hadar da AM da kuma FM.
Rundunar Yan Sanda ta Kano ta Bayyana Sunayen Mutane 72 da Ta ke Nema Ruwa A Jallo
Kawo wannan lokaci dai gwamnatin ba tayi karin haske ba kan dalilin dakatarwar.

Kafin wannan nadi da aka yiwa, Abubakar Adamu Rano, yayi aiki a kafafen yada labarai kamar Gidan Rediyon Tarayya Pyramid F.m, Guarantee Radio da kuma Nasara Radio. Sannan kuma ya kasance Mataimakin Shugaban gidan Rediyon na Kano (DMD) na yan kwaniki, kafin daga Bisani Ya Zama MD.
Kazalika Shi ne Mamallakin wani Shafi Mai Suna Dalla-Dalla dake yanar Gizo Wato Internet.