Jam`iyyar APC mai mulkin a Najeriya, ta ce nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu a Kotun Koli nasara ce ga dimokuraɗiyya da kuma al`ummar Najeriya.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje shi ya bayyana haka a hira da BBC.
Ya ce wannan nasara ce ga Najeriya ba APC ko sauran jam’iyyu kaɗai ba.

“Ƴan siyasa sun yarda a koma ɓangaren shari’a domin bin kadinsu maimakon a tayar da yamutsi. Dole mu gode wa ƴan hamayya da kuma kowa da kowa,” in ji Ganduje.
Da dumi-dumi: Kotun ta Hana Gwamnatin Kano Kama Musa Iliyasu Kwankwaso
Shugaban jam’iyyar ta APC ya ce da ma sun san nasara tasu ce saboda sun ga alamun haka tun da farko.
“Mun ƙara samun ƙwarin gwiwa da wannan nasara da muka yi a Kotun Koli,” in ji shi.
Ya ce gwamnatinsu za ta ci gaba da ayyukan raya ƙasa da ta faro ba kama hannun yaro.
Hadiman Buhari sun fara yiwa Rarara Martani
Ya yi kira ga sauran jam’iyyu da ƴan takara da cewa su zo a haɗa kai wajen ciyar da ƙasa gaba.

A jiya Alhamis ne Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron korafin zaɓen shugaban ƙasa ta yanke cewa Bola Tinubu ne ya samu nasara a zaɓen shugaban kasa na watan Fabrairun 2023.