Da dumi-dumi: Kotun ta Hana Gwamnatin Kano Kama Musa Iliyasu Kwankwaso

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Babbar kotun tarayya dake zaman ta a jihar kano ta bada umarnin hana kama wanda ya shahara nan wajen yiwa gwamnatin jihar kano ta jam’iyyar NNPP adawa Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito, tun bayan da kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan kano ta ce Nasiru Gawuna ne gwamnan Kano ba Abba Kabir Yusuf ba, Musa Iliyasu Kwankwaso yake yiwa gwamnatin bankada tare da yin wasu zarge-zarge na cewa gwamnatin tana ranto kudaden domin ta tafi ta bar su da biyan bashi.

Talla

Musa Iliyasu Kwankwaso ne dai ya shigar da karar gwamnatin jihar kano da kwamishinan yan sanda na jihar kano, tare da rokon kutun da ta hana wadanda yake kara kama shi har sai kotun ta ji bahasin dalilin da yasa suke son kama shi.

Hadiman Buhari sun fara yiwa Rarara Martani

A cikin Umarnin kotun mai kwanan watan 25 ga watan October, 2023, Kotun ta bukaci wadanda ake kara da kada su kama mai Kara (Musa Iliyasu Kwankwaso) , sannan kowa ya tsaya a matsayinsa har sai kotun ta sauraren dukkanin bangarorin Shari’ar.

Kotun dai ta ce zata fara sauraron karar ne a ranar 07 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Talla

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NURTW ta Karrama DMD Karota Auwal Aranposu

Hukumar dake lura da zirga-zirgar ababa hawa ta jihar...

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...