Daga Rahama Umar Kwaru
Kotun kolin Nigeria ta sanya ranar Alhamis domin yanke hukunci kan karar da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da na Labour, Peter Obi suka shigar.
Mutanen biyu suna rokon kotun kolin ne da ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke wanda ta tabbatar da zaben shugaban kasa Bola Tinubu.

Daraktan yada labarai na Kotun Koli, Dokta Festus Akande, a wata sanarwa a ranar Laraba ya ce an sanya ranar yanke hukunci kan kararrakin.
Kwamitin Gwamnatin Kano na tantance ma’aikatan da Ganduje ya dauka aiki ya mika rahotansa
Ya ce, “Gobe, Alhamis 26 ga watan October 2023, aka sanya domin yanke hukunci kan karar da Atiku da Peter Obi suka shigar suna ƙalubalantar nasarar Shugaban kasa Bola Tinubu.”