Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kwamitin da gwamnatin jihar kano ta Kafa domin tantance ma’aikatan da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta dauka aiki a ƙarshen wa’adin gwamnatin ya kammala aikinsa tare da mika rahotonsa ga gwamnatin jihar.
Idan dai za a iya tunawa, kadaura24 ta rawaito an kaddamar da kwamitin ne a ranar 16 ga watan Agusta, 2023 tare da ba da umarnin sake duba yadda aka dauki ma’aikata 10,800 da gwamnatin Ganduje ta dauka aiki.

A lokacin gwamnati mai ci tace ta gano cewa irin wannan atisayen ne kadai zai magance yadda aka Saka San rai da karya ka’idojin gwamnatin wajen ɗaukar mutanen aiki.
Ya Kamata Mataimakan Gwamnoni a Samar musu da aiki a Kudin Tsarin Mulkin Nigeria- Ganduje
Da yake gabatar da rahoton ga sakataren gwamnatin jihar Dr. Abdullahi Baffa Bichi, shugaban kwamitin, Dakta Umar Shehu Minjibir (Garkuwan Minjibir) ya ce a yayin aikin tantance ma’aikatan sun gano ma’aikata 13,916 aka ɗauka aiki sabanin 10,800.
A cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na hukumar Ma’aikatan jihar kano Musa Garba ya sanyawa hannu, ya ce daga cikin wannan adadi (13,916) ita ma’aikata 12,566 suka tantace, yayin da sauran ma’aikatan 1,350 ba su bayyana ba ko kuma sun gabatar da kansu a gaban kwamitin ba .
Dokta Shehu Minjibir ya bayyana cewa, kwamitin ya yi cikakken bayani kan lamarin tare da bayar da shawarwari masu inganci wadanda suka dace da ka’idojin da aka shimfida, don haka ya bayyana fatan gwamnatin jihar za ta yi amfani da shawarwarin.
A nasa jawabin, sakataren gwamnatin jihar Dr. Baffa Bichi, yayin da yake godewa mambobin kwamitin bisa kyakkyawan aiki da suka yi, ya ce gwamnatin jihar za ta duba bayanan da suka gabatar da nufin yin abin da ya kamata.

Ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta yi adalci yayin da take yanke shawara kan shawarwarin da aka bayar. Domin kuwa gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf tana bada fifiko ga ma’aikatan gwamnati .