Daga Kamal Yakubu Ali
Wata Baiwar Allah ta karbi addinin musulunci karkashin jagoranci Shahararren dan kasuwar nan Alhaji kabiru sani kwangila Yakasai Khadimun Nabiyy.
Mrs Ekechi ta karbi addinin musulunci ne a wajan taron mauludin Annabi sallallah Alaihi wasallam na mako-mako da ake gabatar karkashin jagoranci khadimun Nabiyyi Alhaji kabiru sani kwangila Yakasai.

Elechi ta bayyana cewa ta yanke shawarar karbar addinin musulunci ne saboda ta fahinmci cewa shi ne addinin da Allah ya yarda dashi, kuma shi ne zai tseratar da mutum a rayuwar duniya da lahira.
Tace sun zo ne tare da tsohon mijinta wanda daman shi ya kasance musulmi ne, wanda ya dade yana kwadaitar da ita game da addinin musulunci wanda hakan yayi sanadiyar rabuwarsu, inda yanxu ta yanke shawarar karbar addinin musulunci.
Yadda Wani Saurayi Da Budurwa Suka Daurawa Kansu Aure A Jigawa
Sheikh Barrister Habib Muhammad Dan Almajir Fagge shi ne wanda jagoranci bata kalmar Shahada ya taya ta murna game da baiwar da Allah yayi mata na karbar addinin musulunci, sannan ya bayyana mata cewa yanxu ta zama kamar cikakkakiyar musulma kuma dukkannin Laifukan da tayi a baya Allah ya gafarta mata.
A Karshen Ekechi wadda ta bukaci a sanya mata suna Halima domin domin samun albarkacin. Ai suna kasancewar taji Tarihin wannan baiwar Allah, da irin gudunmawa da ita baya musulunci da musulmi.

Wakilinmu Kamal Yakubu Ali ya bamu labarin cewa Taron ya gudana a farfajiyar Gidan Alhaji munzali sani Musa.