Doguwa/Tudun Wada: Kotu ta yanke hukunci kan Shari’ar Alhassan Ado Doguwa da Salisu Yusha’u

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya samu nasara a karar da Salisu Yushau Abdullahi na Jam’iyyar NNPP ya shigar gaban kotun daukaka kara, wanda yake neman a soke zaben dan majalisar Doguwa/Tudunwada da aka sake a yankin.

Da yake yanke hukunci a karar da Abdullahi ya shigar a kan dan takarar jam’iyyar APC, Justice L.B. Owolabi, ya ce wanda ya shigar da karar ya gaza gabatar da gamsassun hujjoji ga kotun.

Talla

Mai shari’a Owolabi ya ce duk wasu dalilai guda uku da mai shigar da kara ya dogara da su – kamar su, zargin da Doguwa da yin Almundahanar kuri’u, rashin bin dokar zabe, da rashin samun kuri’un da ake bukata na halal, ba su da tushe balle makama kuma ba za a amince da su a matsayin dalilan soke zaben ba.

Kotun Kolin Nigeria ta Bayyana Matsayarta Kan Batun Takardun Tinubu

Dangane da zargin tashe-tashen hankula a lokacin zabe, shaidu 21 na mai shigar da kara sun ba da shaida akasin abun da Mai Kara ya ke kara, inda suka bayyana cewa ba a samu wani tashin hankali ba a lokacin zaben.

Kotun, a cikin hukuncin da ta yanke, ta amince da cewa dukkan shaidu 32 da mai shigar da kara ya kira, sun kasa bayar da kwakkwarar hujjar da za ta iya gamsar da kotun har tasa a sake zaben.

A lokacin da yake gabatar da hukuncin, alkalin kotun ya yi mamakin yadda dukkanin shaidun mai shigar da kara suka isa rumfunan zabensu daban-daban a lokaci guda kuma suka shaida yadda akai aringizon kuri’u a mazabun nasu, amma suka kasa gane takardar sakamakon zaben. Don haka shaidun basu gamsar da kotun ba.

Talla

“Mai shigar da kara gaba daya ya gaza tabbatar da shaidun da zasu sa a rushe zaben da ya baiwa Alhassan Ado Doguwa nasara, don haka kotun ta tabbatar da cewa Doguwa shi ne ya lashe zaben da kuri’u mafi rinjaye,” inji alkalin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NURTW ta Karrama DMD Karota Auwal Aranposu

Hukumar dake lura da zirga-zirgar ababa hawa ta jihar...

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...