Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Hukumar tace Fina-finai da dab’i ta jihar Kano tace zata hada hannu da ma’aikatar shari’a ta Kano domin ladaftar da masu karya dokokin hukumar dan a tsaftace harkar Masana’antar tare da kawo mata cigaba mai dorewa.
“Na zo ma’aikatar shari’a ne dan na kawo muku kwafin sababbin dokokin da hukumarmu take so ta kara tare da zamanantar da tsofaffin dokokin da take aiki dasu domin suyi dai-dai da zamani da ake a ciki yanzu”. Abba El-Mustapha

A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, yace shugaban hukumar tace fina-finan Abba El-Mustapha ne ya bayyana haka a yayin wata ziyarar taya murna tare da karfafa alaka a tsakankanin hukumomin Biyu.
Kwankwaso ya Taya Ganduje Murnar zama Shugaban APC na Ƙasa
Shugaban hukumar tace fina-finan ta kano yace mafi yawan dokokin da hukumar take aiki dasu a halin yanzu na bukatar sauyi ko kuma ayi musu gyara don su dace da wannan zamanin
Shi ma anasa jawabin Kwamishinan ma’aikatar Shari’a ta jahar Kano, Barr. Haruna Isah Dederi ya yabawa Shugaban hukumar tace fina-finan Abba El-mustapha dan gane da kokarin da yake naganin hukumar ta cimma wani mataki wanda zai bunkasa aiyukan hukumar.

“Kofar mu abbude take domin bayar da dukkan shawarwarin da zasu taimaki hukumar tace fina-fina domin sabuntawa da samar da dokokin da zasu kara inganta aiyukan hukumar”. Inji Dederi
Kwamishinan ma’aikatar Shari’ar ta kano, ya kuma nuna farin cikin sa dangane da ziyarar da Alh. Abba El-mustapha ya kai musu a matsayin sabon Shugaban hukumar tace fina-finai da dab’i ta jahar Kano domin jaddada alaka tare da neman yin aiki tare.