Mun soke lasisin kowa a Kannywood – Gwamnatin Kano

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Shugaban Hukumar tace fina-finai ta Kano Abba El-mustapha yayi karin bayani kan dalilan gwamnati na soke lasisin yan masana’antar Kannywood.

 

” Mun ɗauki wannan matakin ne domin Muna bukatar musan su waye jarumai, su waye masu shirya fim da masu bada umarni da sauran wadanda suke bada gudunmawa a masana’antar Kannywood don tsaftace harkar ba don mu cutar da su ba”.

Muna da yaƙinin Abba El-Mustapha zai kawo gyara a Kannywood – Baban Nura

Abba El-Mustapha ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a Kano.

Talla

Shugaban hukumar ya ce zasu tantance dukkanin rukuni 13 da suke bada gudunmawa a masana’antar Kannywood, domin fitar da baragurbi da suke lalata sunan Masana’antar a idon duniya.

Yanzu-Yanzu: Sojojin Nijar sun Bayyana Sabon Shugaban Kasar

” Zamu yi aikin ne da dukkanin kungiyoyin da suke Masana’antar Kannywood domin su suka san kowa , don haka zasu taimaka mana wajen saukakawa mana wajen gudanar da aikin tantancewar”. Inji El-Mustapha

Ya kuma bayyana cewa hukumar ta dakatar da duk gidajen gala dake jihar kano tare da umartar Masu gidajen da masu wasan da su halarci hukumar tace fina-finai don tantancesu da Kuma sanin hakikanin masu yin harkar.

Hakan nan Abba El-Mustapha yace daga ranar litinin mai zuwa hukumarsa ta dakatar da sakin duk wani fim din India ko America da aka fassara da harshen Hausa, yace sun dau matakin ne saboda suna da burin tsaftace harkar.

” Suma masu harkar sayar da magungunan gargajiya a tituna da kasuwanni muna umartarsu da su dakata har sai sun kawo mana kaset din da suke sakawa don tantancewa, domin magance kalaman batsa da wadanda basu dace ba”. A cewar Abba El-Mustapha

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Tinubu ya ba da Umarnin rage kudin aikin Hajjin 2026

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumar kula...

Hukumar yaƙi da cin-hanci ta jihar Kano ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da Naira biliyan 4 a Kano

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da...

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics ta Yi Allah-wadai da Yunkurin Siyasantar da Bikin Cikar Najeriya Shekara 65 a Kano

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics (FPA) ta yi Allah-wadai...

Yan Uwa da Abokan Arzikin Sabon Kwamishinan Shari’a na Kano Sun Shirya masa addu’o’i na musamman

Yan uwa da abokan arziki na kwamishinan shari'a na...