Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben jihar Adamawa.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi.
Jami’in tattara sakamakon Hudu Ari ya ayyana Sanata Aisha Dahiru wacce aka fi sani da Binani a matsayin wadda ta lashe zaben bisa wasu yanayi da ake ta cece-kuce akan su.
Amma Festus Okoye, mai magana da yawun INEC, yace an soke zaben tare da bayar da umarnin dakatar da tattara sakamakon zaben.
Daily trust