Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya nemi afuwar al’ummar jihar kano sakamakon karewar wa’adin gwamnatin sa.
” Na yafewa duk wanda ya taba fadar wata magana akai na , Kuma nima Ina rokon ku da ku yafe min duk laifukan da nayi muku, tunda dama Malam yanzu ya fadi muhimmancin yafiya a addinin musulunci”. Ganduje
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da ya halarci Tafsirin Al’qur’ani mai girma a masallacin juma’a na alfur’qan dake Nasarawa GRA kano.
” Wa’adina ya zo ƙarshe a mulkin jihar kano Ina yi muku bankwana, ina yi muku fatan alkhairi, kuma wadanda muka batawa ku yafe mana, nima na yafewa duk wanda ya fadi wani abu akai na ko meye na yafe masa” . Ganduje ya jaddada
Ganduje dai ya mulki jihar kano tsahon shekaru 8 tun daga Shekara ta 2015 zuwa ƙarshen watan gobe 29 ga watan mayun 2023.