Rundunar ƴan sanda a Kano ta ce ta kama mutum huɗu da ake zargi da yunkurin ƙona ofishin hukumar zaɓe a karamar hukumar Takai na jihar.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun ƴan sandan jihar SP Abdullahi Kiyawa ya fitar, ta ce ana zargin mutanen huɗu da yunkurin ƙona ofishin na INEC a daidai lokacin da ake sanar da sakamakon zaɓe.
BBC Hausa ta rawaito Sanarwar ta ce ƴan sandan sun samu nasarar kama mutanen ne bayan kai samamen gaggawa tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro.
Haka ma, ƴan sanda sun ce wasu ƴan bangar siyasa sun kai hari kan ofishin yakin neman zaɓe na jam’iyyar NNPP a karamar hukumar Tudun Wada, inda aka kashe mutum biyu.