Daga Sulaiman Auwal Marshall
An samu rashin amincewa da sakamakon Kanann hukumomin Dambatta da Makoda yayin da ake gabatar da sakamakon zaben shugaban kasa a Hukumar zabe ta kasa reshen jihar Kano.
Wakilin Jam’iyar NNPP game da sakamakon zaben shugaban kasa Rabiu Gwarzo yayi korafin cewa ba’ayi amfani da Na’urar BVAS ba yayin gudanar da zaben.
Sai dai da yake mayar da Martani wakilin Jam’iyar APC a zaben shugaban kasa Rabiu Sulaiman Bichi yaki amincewa inda yace Jam’iyar sa ta baiwa NNPP tazarar kiri’u sama da dubu 2 ba kamar yadda baturen zaben ya bayyana ba.
A sakamakon zaben daya fita a hukumance Jam’iyar APC ta samu kuri’u dubu 12 da 590 yayin da Jam’iyar NNPP ta samu kuri’u dubu 12 da 247 a karamar Hukumar Makoda sai kuma APC ta samu dubu 13 da 179 yayin da Jam’iyar NNPP ta samu kuri’u dubu 15 da 179.
Da yake jawabi babban jami’in Hukumar zabe ta kasa game da zaben shugaban kasa a jihar Kano Farfesa Lawan Sulaiman Bilbis ya bukaci bangarorin biyu dasu kwantar da hankulansu inda ya bukaci a sake komawa domin bin diddigin sakamako zaben na Dambatta da Makoda.