Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Jihar Ekiti da ke kudu mao yammacin Najeriya ta kasance jiha ta farko da ta fara gabatar da sakamakonta na zaben shugaban ƙasar da aka gudana ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu.
Shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmood ya bayar da dama ga babban jami’in haɗa sakamakon zabe a jihar ta Ekiti domin gabatar da sakamakon a zauren tattara sakamakon dake Abuja
Babban jami’in lura da zaben jihar ta Ekitin ne ya jagoranci gabatar da sakamakon kamar haka:
APC – 201,494
PDP – 89,554
LP – 11,397
NNPP – 264
SDP – 2011
Sakamakon ya nuna cewa jami’iyyar APC ce ta samu nasara a zaɓen na jihar Ekiti.
Sai dai babban jami’in hada sakamakon zaɓen ya ce an soke zabe a wasu mazaɓu biyu saboda wasu matsaloli guda biyu da suka hadar da:
Tangardar na’urar BVAS
Da kuma samun adadin mutanen da suka kada kuri’a a mazabar ya zarta adadin mutanen da na’uar BVAS ta tantance