Daga Halima Musa Sabaru
Abubakar Kabiru Abubakar na jam’iyyar APC ya lashe zaben dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi ta jihar kano.
Baturen zaɓen da hukumar zabe ta kasa INEC reshen jihar kano ta tura Bichi Farfesa Sunusi Sani Adamu ne ya bayyana sakamakon zabe a karamar hukumar Bichi.
Baturen zaɓen ya ce Abubakar Kabiru Abubakar ne ya lashe zaben Inda ya sami kuri’u 38,943 wanda hakan yake nuna shi ne ya Sami kuri’u mafi rinjaye cikin zabukan yan takarar Jam’iyyu 8 da suka shiga zaben .
Ga sakamakon zaben