Ina jan kunnen masu ‘yaɗa jita-jitar kafa gwamnatin riƙon kwarya a Najeriya – Buhari

Date:

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta ce babu ƙamshin gaskiya cikin kalaman da ake yaɗawa kan cewa Muhammadu Buhari na shirin miƙa mulki ga gwamnatin riƙon ƙwarya.

 

Cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan lamuran yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya ce, “ya kamata a daina ɗaukar lamarin gwamnatin riƙo da wasa, maganar zaɓe na nan daram.”

Talla

Yayin da aka jiyo wasu shugabannin na zargin cewa Shugaba Buhari na neman daƙile kafafun dimokradiyyar Najeriya, a wani gefen kuma iƙirari ne kan cewa ƙarancin naira da ake fama da shi a Najeriya wani ɓangare ne na janyo koma baya ga zaɓe mai zuwa da za a gabatar nan da kwanaki, da kuma shirin miƙa iko ga gwamnatin riƙo.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

A nasa martanin kakakin shugaban ƙasar ya ce wannan wani salo ne mai cike da haɗari da wasu mutane suka ɗauka waɗanda suke ganin za su iya faɗuwa zaɓen.

 

Ya ƙara da cewa ƙirƙiro yanayin da zai jefa mutane cikin firgici ba hanya ba ce da za ta kawo ƙarshen damuwar da aka shiga ba ta sauyin naira.

 

Yace sauyin kuɗin ba a ƙirƙiro shi ba ne domin ya bai wa shugaban ƙasa damar zama a kan karagar mulki har bayan 29 ga watan Mayu, yana cewa “fadar shugaban ƙasa a shirye take ta miƙa mulki ga duk wanda ya ci zaɓe domin gadar Shugaba Buhari.

 

Kuma za a yi hakan ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023 kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Likitocin Jinya da Ungozoma sun janye yajin aiki – Ministan lafiya

Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta...

Sarkin Hausawan Arewa, Amb. Balarabe Tatari, Ya Aike da Sakon Ta’aziyyar Buhari da Dantata

Sarkin Hausawan Arewa kuma Ambasadan Zaman Lafiya, Alhaji Balarabe...

INEC ta sanya ranar fara rijistar masu zabe a Nigeria

Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan...