Zaben 2023: Fadar Shugaban Kasa na Goyon Bayan Atiku – Wike

Date:

Daga Aliyu Abdullahi Fagge

 

Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers a ranar Juma’ar da ta gabata ya yi ikirarin cewa fadar shugaban kasa tana goyon bayan Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben dake tafe nan da makwanni uku masu zuwa.

 

Wike ya bayyana hakan ne a garin Ibaka da ke tsibirin Okrika yayin gangamin yakin neman zaben jam’iyyar PDP na karamar hukumar Okrika a jihar Rivere.

Talla

Ya kuma ƙalubalanci sauyin kudin naira da aka yi, Inda yace a matsayin su na yan adawa suna bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake duba batun aiwatar da manufofin.

 

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

 

Ya kara da cewa Atiku da magoya bayansa a kwanakin baya sun bayyana cewa ba sa bukatar Gwamnonin G-5 kafin su ci zabe, Saboda goyon bayan wasu mutane da suke samu daga fadar shugaban kasa.

 

 

A cewarsa, “Su (Atiku da magoya bayansa) suna ganin an ba su tabbacin zasu ci zabe, amma Ina so su sani zaben bana mutane ne zasu yanke hukunci ba wai wasu mutane a fadar shugaban kasa ba.

 

 

Dangane da batun sabon tsarin kudin, gwamnan Rivers ya ce, “Wannan manufar ta musgunawa mutane ce, inda yace mutane da kudaden su a bankuna amma an hana su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...