Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi barazanar soke amincewar da yayi na bada filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke Fatakwal, domin gudanar da taron yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.
Wike ya ce babban daraktan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a jihar, Dr. Abiye Sekibo, ya kasance yana yawan ziyartar wurin taron wata guda kafin ranar 11 ga watan Fabrairu da aka basu domin gudanar da taron.

Gwamnan ya bayyana cewa sun amince Atiku Abubakar ya gudanar da taron ba tare da sun biya ko sisin kwabo ba, amma daraktan yaƙin neman zaben Atikun na Ribas yana ta sintiri a filin bayan kuma za’a basu filin wasa ne sa’o’i 48 kafin taron.

Wike, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a a lokacin da yake jawabi a taron kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar PDP reshen jihar Ribas a karamar hukumar Oyigbo, ya ce Sekibo ba shi da hurumin yin sintiri a filin wasan wata daya kafin ranar da aka kayyade.
Wike ya gargadi Sekibo da kada ya harzuka gwamnatin jihar Ribas ta janye amincewar da akai na basu filin wasan na jihar makonni kadan kafin zuwa ranar da zasu gudanar da yakin neman zabe, in ba haka ba za a soke amincewar.