Daga Ibrahim Sani Gama
An shawarci kungiyar ma’aikatan gidajen rediyo da talbijin da harkokin wasan kwaikwayo ta kasa da su kara jajircewa domin nemawa yan kungiyar hakkokinsu domin ciyar da kungiyar gaba.
Shugaban kungiyar kwadago na jihar kano kwamaret kabiru Ado munjibir ne ya ba da wannan shawarar a lokacin gudanar da zaben sabbin shugabanni kungiyar ta Rattawu ta jihar kano, wanda ya gudana a helkwatar kungiyar ma’aikatan lafiya dake unguwa uku yan Awaki a nan kano.
Kwamaret minjibir yace kungiyar kwadago ta jihar kano a shirye take domin yin aiki kafada da kafada da Sabon shugabancin kungiyar Rattawu wajen nemawa ma’aikata hakkokinsu, musamman yan fansho da suka kammala aiki ba, a biyasu hakkokinsu ba da kare mutuncin ma’aikata a kodayaushe.

Shugaban kungiyar Rattawu na kasa kwamaret kabiru bello tsanni, wanda mataimakin kungiyar na Arewa maso yamma kwamaret Abubakar chika ya jagoranta, yace sun fito da Managartan tsare tsare na horas da yan kungiyar da neman hanyoyin gyara musu albashin yan jarida na rediyo da talbijin da kawo sabbin ayyukan da za su inganta ayyukan Yada labarai a koina a fadin kasar nan.
Ya shawarci wadannan sabbin shugabanni da su tallafawa kungiyoyinsu ta hanyoyin da suka kamata domin ciyar da kungiyar gaba.

A jawabinsa Sabon Shugaban kungiyar Rattawu na jihar kano kwamaret Babangida mamuda Bilyaminu ya godewa yan kungiyar bisa zabarsa da suka yi inda ya sha alwashin aiwatar da aiki yadda ya kamata domin ciyar da kungiyar gaba.
Hajiya samira Hassan ita ce ta lashe kujarar jami’ar hulda da jama’a ta kungiyar Rattawu reshen jihar kano, wadda ta lashe zabenta babu hamayya a karo na biyu, ta kuma yi alkawarin yin aiki tukuru wajen ganin an ciyar da kungiyar gaba.

Ta yabawa yan kungiyar ta kasa da ta jiha dangane da goyan baya da suka bata wajen dawowa matsayin ta a karo na biyu, inda ta ba da tabbacin gudanar da aiki cikin gaskiya da rikon Amana.