Sarkin Kano ya halarci taron murnar cikar Nigeria 62

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya halarci taron murnar cika Shekara 62 da samun yancin kan Najeriya.

Taron an gudanar dashi ne a filin wasan kwallon kafa na Sani Abacha dake kofar Mata a cikin birnin Kano bisa jagorancin Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam.

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero wanda shine Shugaban Majalisar Sarakunan Kano ya kasance a wajan taron tare da Masu Martaba Sarakunan Bichi da Rano da Gaya da Kuma Karaye.

Talla

An dai Gudanar da taron ne tare da faretin ban girma daga Jami’an “Yan Sanda dana hana fasakori dana hana shige da fice da kuma na kula da gidajen gyaran hali.

Talla

Sauran jami’an da suka gudanar da faretin sun hadar dana kula da ababan Hawa ta jihar Kano da sauran kungiyoyin addini da Yan makaranta.

Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Chief Press Secretary to Kano Emirate Council.
01/10/2022

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...