Daga Aisha Aliyu Umar
Shugaban kungiyar tsofaffin daliban makarantar firamare ta Jangaru dake Kunture a karamar hukumar ungoggo a jihar kano Abubakar jibril yayi kira ga gwamnatun jihar kano da masu rike da madafun iko a karamar hukumar dasu taimakwa makarantar jangaru da kayan koyo da koyarwa domin inganta ilimin yaran dake yankin.
Yace a bayan kunguyarsu ce take taimakawa makarantar da kayan karatu da kuma abun zaman dalibai da dai sauransu , amma yanzu yace lamarin yafi karfin su dole sai gwamnati ta shigo don tallafawa ilimin daliban makarantar.
“Yanzu haka wannan makarantar firamare ta jangaru tana bukatar samun sabbin ajujuwa, sannan tana bukatar a gyara na baya da ake dasu, saboda mafi yawa daga cikinsu idan akai ruwan sama basa shiguwa saboda yadda ruwa yake zuba a cikinsu”. Inji shugaban kungiyar
Mun sani gwamnati tana kokari wajen inganta ilimi a jihar kano, kuma dole a yaba mata saboda irin kokarin da take yi hakan tasa muka ga dacewa yin kira da babbar murya da a kawowa makartarmu daukin gaggawa ko dan kannenu da ‘yayanmu suma su shaida kokarin da ake na inganta ilimi a kano.
” Wannan makaranta ta Jangaru firamare da ke unguwar kuntire karamar hukumar Ungoggo tana bukatar kayan karatu bandakuna office din malamai na maza dana mata bencinan yara da dai sauransu”. Inji Abubakar