Duk lalacewar PDP gwara ita da jam’iyyar APC — Kwankwaso

Date:

 

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin mafi lalacewa cikin jam’iyyun siyasa a wannan lokaci, dukda dai yace itama PDP ba kanwar lasa bace wajen kama-karya a yanzu, domin duk cancantarka da haƙƙin ka, zaka iya rasa shi ta dalilin wasu sojojin gona.

Kadaura24 ta rawaito cewa, Kwankwaso ya bayyana haka ne jiya Lahadi, yayin taron masu ruwa da tsaki na Kwankwasiyya a gidansa dake Kano, inda yace har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP, amma shirye-shirye sunyi nisa a tsakaninsa da jam’iyyar NNPP mai kayan marmari.

Kwankwaso yace fita daga jam’iyya da komawa ba illa bane, kuma hakan ma shi ne kwarewa a siyasa, domin a shekarar 2018 da sukayi zaben fidda gwani a Fatakwal, wadanda suka zo na farko, na biyu, na uku dana hudu, duk sunbar PDP sun dawo, sai kuma wasu tarkace da suka biyo baya, a cewar Kwankwaso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da Ɗumi-Ɗumi: Labarin da ake yadawa kan matsayar siyasa ta ba gaskiya ba ne – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya yi...

Da dumi-dumi: Gwamnatin Kano ta Haramta “Kauyawa Day”

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Hukumar tace fina-finai da dab'i ta...

Inganta ilimi: Shugaban Karamar hukumar Ungoggo ya kaddamar da rabon kayan koyo da koyarwar

Daga Shehu Usaini Getso Shugaban karamar hukumar Ungoggo Alhaji Tijjani...

Karyewar gada ya jefa dubban al’umma cikin mawuyacin hali a Rano, Sun nemi Agajin Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim Al’ummar garuruwan Kazaurawa/Unguwar Ganji da ke...