2023: Al’ummar Kano ta Kudu sun amince zasu goyi bayan Alhassan Rurum a matsayin Gwamna, Kawu Sumaila kuma Sanata

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali
Kungiyar cigaban Kano ta kudu Wato Kano South Concern Citizens Forum (KSCCF) ta amince zata goyi bayan Hon.Kabiru Alhassan Rurum ya zama gwamna a shekara ta 2023 don maye gurbin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
 Kadaura24 ta rawaito Alhassan Rurum, Wanda tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano ne a zamanin Ganduje na farko, kuma a halin yanzu mamba ne mai wakiltar mazabar Rano, Kibiya da Bunkure kuma shugaban kwamitin fansho na majalisar wakilai ta Kasa.
 Kungiyar ta kuma amince da Hon.  Kawu Sumaila ya Zama sanatan da zai wakilci Kano ta kudu, shi kuma Hon. Alhassan Ado Doguwa ya sake zama dan majalisar wakilai Mai wakiltar Tudun Wada/Doguwa domin ya samu damar zama kakakin majalisar.
 Da yake karanta sanarwar da kungiyar ta rabawa manema labarai bayan zamanta a Kano ranar Lahadi a madadin shugaban kungiyar Sen Mas’ud El-jibrin Doguwa tsohon Sanatan Kano ta Kudu, Alh.Musa Salihu ya ce Kano ta Kudu ta cancanci ta sami kujerar siyasa mafi tsoka a kano.
 Salihu ya kara da cewa, Kano ta Kudu ba ta samu damar samar da gwamna a jihar kano ba tun 1992, yana mai cewa, “Kano ta Kudu tana da manya-manyan kananan hukumomi har guda 16 a Kano.”
 Alh. Musa Salihu ya ce, “Kano ta arewa da Kano ta tsakiya sun samar da gwamnoni. A shekarar 2023 ya kamata a mayar da Kujerar mukamin gwamna zuwa Kano ta Kudu domin ta samu kaso mai tsoka na Kujerar Gwamna”.
 Salihu ya ce Kano ta Kudu na da muhimmiyar rawar da za ta taka wajen gina jihar Kano, yana mai cewa shiyyar a shirye ta ke ta bayar da iyakacin kokarinta don ganin an cimma wannan manufa.
 Ya kara da cewa, “Don haka muna goyon bayan Alhassan Rurum a matsayin gwamna a 2023 domin ya gaji Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
 “ Da yake muna duba cancanta ne mun Amince , Hon.Kawu Sumaila ya zama Sanata Kano ta Kudu shi kuma Hon. Alhassan Ado Doguwa a sake zabensa a matsayin mamba Tudun wada da Doguwa domin ya samu damar zama kakakin majalisar wakilai ta kasa.”
 Sai dai nan ba da jimawa ba Kungiyar zata kira taro da wadanda aka amince da su domin bayyana musu matsayinsu.
 Wadanda suka halarci taron sun hada da Farfesa Abdu Salihi, Farfesa Isa Yahaya Bunkure, Galadiman Karaye, Alh. Surajo Garba Karaye, AIG Zarewa, Dr. Aisha Isyaku Kiru, Hon. Alhassan Abubakar Tsohon Kakakin Majalisar dokokin jihar Kano, Hon.  Abdullahi Maraya, tsohon Mataimakin Kakakin Majalisa, Limamai da Malamai daga Kano ta Kudu, kungiyoyin dalibai da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Na sauke nauyin da Tinubu ya ɗora min – Gwamnan riko na jihar Rivers

Vice-Admiral Ibok-Ete Ibas (Mai ritaya), wanda shi ne gwamnan...

Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi: Kawu Sumaila ya jinjinawa Gwamnan Kano

Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar...

Gwamna Yusuf Ya Shirya Baiwa Kananan Hukumomin Kano Cikakken ‘Yan cin Kai

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...

Majalisar Zartarwa ta jihar Kano ta Amince da kashe Naira Biliyan 18 don aiwatar da wasu aiyuka

  Majalisar zartarwar jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir...