Abba kyari ya musanta zargin safarar Muggan kwayoyi

Date:

Babban jami’in ‘yan sandan Najeriya da aka dakatar ya musanta zargin alakanta shi da kungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ta ƙasa da ƙasa.

An kama Abba Kyari ne a makon da ya gabata bayan da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar NDLEA ta zarge shi da alaƙa da wata kungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi da ke aiki tsakanin Najeriya da Habasha da kuma Brazil.

Sai dai a ranar Litinin ya shaidawa wata kotu a Abuja babban birnin kasar ta hannun lauyoyinsa cewa ƙirƙirar zargin aka yi.

Hukumar NDLEA ta yi zargin cewa Mista Kyari ya yi yunkurin bai wa jami’anta cin hanci don kilo 25 na hodar ibilis da jami’ansa suka kama sannan suka raba.

Amma ya musanta zargin.

Ya ce jami’an hukumar NDLEA ne suka masa gadar zare bayan ya nace sai an bayar da lada ga wanda ya bayar da labarin da ya kai ga kama waɗanda ake ake zargi da safarar miyagun kwayoyi kamar yadda suka amince da farko.

Ɗaya daga cikin lauyoyinsa Hamza Nuhu Dantani, ya shaida wa BBC cewa sun kuma gabatar da bukatar neman belinsa.

Ya ce saboda an ci gaba da tsare shi sama da sa’a 24 ba tare da gabatar da shi kotu ba kan zargin da ake masa, wanda ya saɓa ƴancinsa na ɗan adam.

A ranar Alhamis kotu za ta saurari buƙatar da lauyoyinsa suka shigar na neman beli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...

Al’ummar Kano ku baiwa AA Zaura hadin Kai domin ya kawo karshen fadan Daba – Baba Yawale

Daga Halima Umar Dogo   Babban Hadimin AA Zaura Alhaji Baba...

Gwamnatin Kano ta magantu kan Hukuncin kotu na zaben kananan hukumomi

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Kano ta bayyana farin...