Daga Umar Hussain Mai Hula
Gidauniyar alfajr ta kaddamar da wata sabuwar makaranta Mai suna Alfajr college of education wadda aka Samar da ita domin koyar da Ɗalibai karatu kyauta tun daga farawa har Zuwa Lokacin kammala Makarantar.
Yayin da yake ganawa da wakilin Kadaura24 Jagoran Makarantar Sheikh Abdulkhaliq Elmulla yace an samar da Makaranta ne domin Inganta harkokin addinin Musulunci Musamman Karatun Karatun alqur’ani Mai girma.
Sheikh Abdulkhaliq Elmulla yace Makaranta ta zo da tsarin bada Ilimin alqur’ani kyauta ga Kananan Yara Musamman a tsarinsu na haddace alqur’ani da ka’idojin da Cikin Shekara Guda, Wanda akai Masa Suna (Tajur Wakar).
Yace an samar da Wannan tsari ne da nufin rage kukan da Gwamnati take yi akan yawan Samun Yara mabarata a akan titi, yace idan iyayen Yara Suka gane Shirin zasu daina tura ‘ya’yan su almajiranci.
Sheikh Elmulla ya Kara da cewa akwai tsarin gyarawa mahaddata alqur’ani karatunsu ta hanyar koyawa musu dukkanin wasu ka’idojin alqur’ani da Kuma kira’o’in Guda goma da tafsiri da dai Sauransu Kuma yace shi ma Wannan tsari kyauta ne.
” Muna iya daukar Waɗanda suka iya karanta alqur’ani Karatu kubutacce Musamman a ga Masu shiga tsarin Tajur Wakkar, shi Kuma Daya tsarin dama na mahaddata alqur’ani ne , Waɗannan su ne abubun da ake bukata kafin mu dauki dalibi”. Sheikh Elmulla
Yace akwai tsari na Musamman da suke tinanin fito da shi Musamman ga Waɗanda basu San Baki ba ,domin Suma su shiga Cikin Waɗanda zasu Mori alkhairin da Gidauniyar alFajr ta kawowa al’ummar Jihar Kano.