Wata Kotu a kano ta yankewa wani barawon wayoyi hukuncin daurin wata 6 ko zabin tara

Date:

Daga Ibrahim Aminu Riminkebe
Kotun Magistrate mai lamba 35 dake zamanta a Nomansland karkashin jagorancin Mai Shari’a Mal Ibrahim Al-Mustapha Kofar mata an gabatar da wani matasahi mai suna Nazifi Sunusi dan kimanin shekaru 26 mazaunin unguwar Dabai daka karamar hukumar Gwale wanda ake zarginsa da zuwa unguwar gobirawa cikin karamar hukumar Dala wanda ya haura gidan wani mutum ya sace wayoyinsu kirar Samsung da Techno Wanda kimar kudinsu yakai kimanin dubu Dari da tara.109,000.
Kadaura24 ta rawaito tun da farko dai mai gabatar da kara a kotun Haj, Rabi’atu Sule ce tayi roko ga mai Shari’a da yayi umarnin karantawa Wanda ake tuhuma kunshin tuhume-tuhumen da ake masa da yaren da zai fuskanta, nan take kuwa Mai Shari’a Mal Ibrahim Al-Mustapha Kofar mata ya amince da hakan.
Nan take aka fara karanta masa tuhumar da ake masa na cewar ana zarginka da tsallaka gidan mutane tare da sace musu wayoyinsu, “shin ko ka aikata wannan abubuwan da ake zargin ka dashi ?” yace ai ya mai Shari’a babu wani Ja akan wannan batu na aikata Abinda ake zargin na akai.
Bayan wannan ikirari ne sai mai gabatar da kara Haj. Rabi’atu Sule ta sake rokon wannan kotu da tayi masa hukuncin na nan take.
Bayan gabatar da rokonne mai Shari’a Ibrahim Al-Mustapha Kofar mata ya yankewa wannan matashi hukuncin Daurin watanni shida (6) a gidan gyaran hali sakamakon wadannan laifuka guda biyu, ko kuma zabin tara na Naira dubu Ashirin 20,000.
Haka zalika mai Shari’a Malam Ibrahim Al-Mustapha ya yi umarnin ya biya wadanda ya sacewa wayoyinsu kudinsu wadanda kimar kudinsu yakai Naira dubu Dari da Goma da tara (109,000).
Sannan kuma yayi umarnin da zamanto mai dabi’u nagari a duk inda yasamu kansa.
Daga bisani Jami’in Gidan gyaran hali Mataimakin Sifeto Abbas Abubakar Musa ya tusa keyar Nazifi Sunusi zuwa Gidan gyaran hali domin cika umarnin kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...