Daga Kamal Yakubu Ali
An bayyana tallafawa juna da cewa yana taimakawa wajen Kara so da kauna Tsakanin Mutum da Mutum Kuma Musamman ma Dan uwa na jini.
Sakataren kwamittin gidan malam lasan malam Harazimi ubale ya bayyana hakan yayin Wani Babban taro Wanda zuri’ar Gidan Malam Lasan suka gudanar a Kano.
Malam Harazimi yace suna gudanarda wadannan tarurruka ne domin kara hada kan al’ummar gidan da kuma tallafawa juna ta bangarori daban daban.
Ya kuma kara da cewa sun fara gudanarda da taron ne shekaru arba’in da biyu da suka gabata karkashin jagorancin Alh yusif Nasidi, inda izuwa yanxu sun samu Nasarori da dama .
“Nasarorin da wannan taro ya samar sune an daura Auren mutane goma sha biyu wadanda dukkaninsu jikokin wannan gidane na malam Lasan tare da tallafawa Masu karamin karfi a Cikinmu ,Babu shakka Muna alfahari da Waɗannan nasarorin”. Inji Malam Harazimi
Ya kuma bukaci yan uwa da abokanan arziki dasu bada hadin kai wajan cigaba da kawo cigaba da hadin kai tsakanin zuri’ar gidan na Malam Lasan .
Mutane da dama ne suka halarci taron daga sassan