Rikicin APC a kano: Yau litinin za a fitar da sabon jadawalin Shugabancin jam’iyyar

Date:

A jihar Kano, jam’iyyar APC mai mulki ta wayi gari cikin dakon wani sabon tsarin da uwar jam’iyyar ta kira “wanda zai shigar da kowa a dama da shi” cikin harkar shugabanci.

Duka ɓangarorin biyu, tsagin Sanata Shekarau ko kuma G7, da kuma na Gwamna Ganduje na kira ga uwar jam’iyyar ta tabbatar da adalci.

Jam’iyyar APC ta ce bayan sanar da wannan tsari, za ta kafa wani babban kwamiti da zai je Kano don tabbatar da cikakken aiki da shi.

Tun a shekarar 2021 ne, bangaren gwamna Ganduje da na sanata Shekarau, suka sa zare

Zabukan shugabannin jam’iyya a matakin kananan hukumomi dana mazabu da kuma na Jiha ne suka jefa jam’iyyar cikin wannan rikici.

Har yanzu kowanne bangare na fatan ace shi ne ke jagorancin APC a Kano.

Bayan jerin tattaunawa da uwar jam’iyyar ke shiga tsakani, a karshe ana iya cewa za a sansanta komai.

Tuni wasu jagororin jam’iyyar a Kano suka fara tausar zukatan ‘ya’yan jam’iyyar, kamar sanata Ibrahim Shekarau.

Sanata Shekarau ya shaida wa BBC cewa,a halin yanzu suna jiran karbar wadannan ka’idoji da matakan sulhu daga uwar jam’iyya.

Sanatan ya ce,”Ina kira ga wadanda ke cewa basa son sulhu da su tuna cewa maganar sulhu umarni ne daga Allah (SWA)”.

Ana su bangaren tsagin gwamna Ganduje ta bakin Honourable Kabiru Alasan Rurum, ya ce suna fatan su tsarin da uwar jam’iyyar zata kawo ya mutunta tare da daraja kowanne bangare don samun zaman lafiya da kwanciyar hankain da za su iya tunkarar babban kalubalen da ke gabansu a zaben 2023.

Kano dai babbar jiha ce da APC ta dade tana nanata tasirinta a siyasar Najeriya, abin da yasa APCn ke kara kokari wajen ganin ta hana wannan baraka data kunno kai a jihar kara tsawo da fadi.

To ko wannan haka ta Jam’iyyar APCn zata cimma ruwa? lokaci ne kawai zai raba wannan gardamar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...