2023: Matasa a kano sun bayyana Gwamna Yahaya Bello a matsayin wanda zai ceto Nigeria

Date:

Daga Halima M Abubakar
Wata kungiya mai suna Rescue Nigeria Mission da ke fafutukar ganin Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya zama shugaban kasar Najeriya, ta gudanar da wani tarom mata da matasa a Kano.
 Kadaura24 ta rawaito Shugaban kungiyar Abdul Amat Maikwashewa, ya ce gwamnan jihar Kogi ya bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban matasa a Najeriya ta hanyar kusantar da su ga gwamnatinsa tare da bullo da tsare-tsaren da suka dace ga jama’a domin amfanin su.
 Ya kuma bukaci matasan da kada su bari duk wani dan siyasa da bai cancanta ba kuma dattijo mai neman mukamin siyasa yace shi zai fadi makomar matasan da  suke da kashi 70 cikin 100 na al’ummar kasar nan.
 Abdul Amart ya godewa wadanda suka shirya taron bisa amincewar Gwamnan Yahaya Bello tare da jaddada cewa yana da kwarin gwiwa da karfin kawo karshen matsalolin tsaro da tattalin arziki da kasar ke fuskanta.
 Ya ce idan Yahaya Bello adoza  zai iya kawar da manyan kalubalen da kuma dawo da hayyacin jihar Kogi, bai kamata a sami wani shakku ba akan ko Yahaya Bello Zai iya gyara Najeriya ba.
 Ya ce, “Idan har gwamna zai iya samar da mafita ga dimbin kalubalen da ke fuskantar jihar Kogi, ba mu da shakka zai iya warware Matsalolin Najeriya.  Da farko mene ne matsalar Jihar Kogi?  Jihar Kogi ce kadai ke da iyaka da jihohi 10, ciki har da FCT, wanda hakan ya sa jihar ta zama karamar Najeriya”.
 “Jihar Kogi ta kasance cibiyar aika aiyukan ta’addanci kafin Yahaya Bello ya karbi ragamar jagorancin kasar jihar. Okene karamar hukumarmu ta kasance tana gina masana’antar bam. Harin bama-bamai a majami’u da masallatai da wuraren taruwar jama’a ya kasance a wannan rana sakamakon ayyukan Boko Haram da ISWA kafin wannan gwamnati ta hau mulki.
Mai kwashewa ya Kara da matakan da Gwamna Yahya Bello ya dauk yasa yanzu jihar kogi ta zama jihar da kafi kowacce Jihar Zaman Lafiya Musamman a shiyyar Arewa ta tsakiya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...