Daga Sadiya Muhammad
Majalisar dattawan Najeriya ta cire wani sashe na 84 wanda ake ta cece-kuce daga cikin kudirin gyaran dokar zabe.
Sashin dai ya bayyana cewa dole nr Jam’iyyun Siyasar kasar nan su gudanar da Zaben kato bayan kato a zaben fidda gwani.
Majalisar dattijai ta cire sashin ne a zamanta na ranar Larabar nan, bayan da majalisar dattawa ta rusa kwamitin baki daya domin yin la’akari da yadda gyaran da shugaba Buhari ya yi akan dokar zabe.
Majalisar dattijai ya yi gyare-gyaren da sa wajaba biyo bayan oda ta 87 karamin sashe (C) na damar da doka ta baiwa majalisar dattawan.
Shugaban majalisar dattawan ya ce sauran abubuwan da wasu ‘yan majalisar sukai gyara baza gyara su ma kafin turawa shugaba Buhari kudirin don amincewa.