Baiwa Addini Musulunci Gudunmawa shi ne sirrin Gwamnatin Ganduje – Murtala Sule Garo

Date:

Daga Abdulrashed B Imam

 

Kwamishinan Kananan Hukumomi na jihar Kano Hon Murtala sule Garo ya bukaci al’ummar musulmi dasu kasance Masu maida al’amuransu ga Allah (S.w.t) tare da yiwa kasa Adu’ar zaman lafiya da yalwar arziki kamar yadda a kasan jama’ar Kano da hakan tun da fari.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin bude masallacin juma’a a garin dotsan dake karamar hukumar dawakin kudu a jihar kano .

Cikin wata sanarwa da Mataimaki na musamman ga Shugaban karamar hukumar kumbotso kan harkokin yada labarai shazali farawa ya aikowa kadaura24 yace Kwamishinan Wanda ya Samu wakilcin Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso Hon Hassan Garban kauye farawa ya bayyana cewa gwamnatin ganduje ta maida hankali sosai wajen habbata addinin musulunci hakan tasa take samun nasara a koda yaushe.

Kamar yadda kuka sani Hidimtawa addini shine ta fuskoki da Dama Shine Sirrin Gwamnatin kano karkashin jagorancin Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje, musamman yadda take bada fifiko akan abubuwan da suka shafi addini, Idan akai Duba da yadda Gwamnatin ta Gina masallatan juma’a a lungu da sakon kananan Hukumomi 44 na jihar Nan” inji Garban kauye.

“A sakon sa ga al’ummar garin na `Dosan kwamishinan ya bukace su, Dasu bada Gudunmawar data Dace wajen Hidimintawa addini da Kuma kula da Sabon masallacin amatsayinsu na wadanda zasu fi kowa amfana dashi bayan Gwamnati ta Mika shi garesu. Sannan Kuma Kwamishinan yace kofa a bude take Ga Shugabanin kananan Hukumomi Koda yaushe.

Wanda Kuma Nan take Shugaban karamar hukumar ya bukaci shimfida Interlock a masallacin nan take Kuma kwamishinan yace Kofa a bude take, Wanda Kuma ya baiwa kwamitin masallacin tallafin naira 100,000, Amatsayin Harsashin Tallafawa masallacin Domin cigaba da kula Dashi, ta Hannun Garban kauye.

Da yake nasa jawabin Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Kudu Hon Nasir Ibirahim Matage ya yabawa kwamishinan kananan Hukumomi Murtala Sule Garo Wanda ya Samu wakilcin Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso Hassan Garban farawa, Bisa irin gudunmawar da yake Baiwa karamar Hukumar Koda yaushe musamman ta fuskar addini da Kuma Samar da managartan ayyukan Raya kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...