Daga Rukayya Abdullahi Maida
An shawarci dalibai dasu kasance sun yi amfani da ilimin Al-qur’ani Mai girma ta hanyar da ta dace kasancewar su ne wadanda Allah ya zaba yan kuma Azurtasu da Haddace Al-qur’ani Mai tsarki.
Bayanin Hakan ya fito ne ta bakin Hon. Ali Muhd Rabi’u babban Mai bawa gwamna shawara kan kungiyoyi masu zaman kansu, kana Kuma wakilin Dan majalisar Tarayya na Karamar hukumar Tarauni Hon. Hafizu kawo.
Yace duk Wanda Allah ya zabe shi cikin Waɗanda suka haddace alqur’ani Mai girma ya kamata ya godewa Allah , Sannan ya sake dagewa wajen neman ilimin sauran fannonin addinin Musulci.
Ali muhd Rabi’u na wannan bayanin ne yayin halartar bikin saukar Al-qur’ani na dalibai 30 maza da mata a karo na farko da makarantar madarusatul Darussalam littahafizul Qur’an kundila wadda ta gudana a yau, inda yace kasancewar sai Wanda Allah ya zaba yake azurtawa da samun wannan dama ta sauke babban kundi izu 60 yasa, yake fatan zasu amfani ilimin har karshen rayuwa.
Bai gushe ba Sai da yayi kira ga sauran daliban su zage damtse wajen neman ilimin alqur’ani da na Sauran fannonin addinin Musulci domin su zama Malamai don Ganin sun gadi Waɗanda suka koyar da su.
Ana sa jawabin shugaban makarantar
Sheikh Mansur Ali Baba yace babu abinda zasu ce sai dai godiya ga Allah gami da farin cikin bisa yadda Taron bikin saukar ya kasance.
Kazalika Mal. Mansur ya Kara da cewa karatun addini na cikin Wani hali a yanzu sakamakon yadda iyaye ke wasarere dashi, dukkuwa da cewa Al-qur’ani shi ne littafin da idan Aka sanshi to kuwa duk Wani ilimin da akasa gaba zai zo da sauki.
Karshe yayi kira kan yadda suka riki ilimin marayun yara wadanda Basu da halin biyan kudin makaranta, inda yace ya kamata masu wadata su waiwayi marayu, marasa karfi, kan batun ilimi don Basu gudunmawar.
Inuwa Kabir yaro Dan Shekaru goma Sha Daya tare da Bilkisu Aminu Mukhtar na daga cikin dalibai 30 da suka rabauta da Haddace Al-qur’ani suka Kuma saukeshi, sunyi farin ciki marar misali tare da kira ga Yan uwansu dalibai musamman yara masu tasowa da su dage wajen Neman Ilimi.
Taron saukar ya samu halartar Al’umma da dama daga ciki hadda Alh. Abdullahi jakadan garko, masu rike da madafan iko, iyayen yara da sauran dalibai.