Fadar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta ce shugaban ƙasar lafiyarsa ƙalau bayan an samu rahoton cewa makusantansa sun kamu da cutar korona a ƙarshen mako.
Mai magana da yawun fadar Femi Adesina ne ya bayyana hakan lokacin da ya bayyana ta cikin shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels ranar Lahadi.
Da aka tambaye shi ko Buhari ya killace kansa sai ya ce: “Ina ganin shugaban ƙasa lafiyarsa ƙalau, yana ci gaba da ayyukansa kamar yadda ya saba. Amma idan wani na kusa da shi ya kamu (da korona), zai killace kansa har sai ya warke. Saboda haka shugaban ƙasa yana ci gaba da ayyukansa kamar kullum.”
Game da mutanen da suka kamu da cutar a fadar ta Aso Rock Villa, Adesina ya ce ba zai faɗi sunansu ba saboda bai sani ba.
“Abin da zan ce shi ne ma’aikatan shugaban ƙasa su ma mutane ne…don muna ma’aikatan fadar shugaban ƙasa hakan ba ya nufin ba za mu kamu da cutuka ba…ba ni da ikon faɗar waɗanda suka kamu saboda ban sani ba.
“Garba Shehu ya tabbatar cewa ya kamu amma ya ce ba ta yi tsanani ba. Kuma na yi imanin cewa zuwa yanzu ya kamata ya warke tun da abin ya faru tun Laraba. Saboda haka babu wani abin tashin hankali.”