Buhari ya yi Bikin Cikarsa Shekaru 79 da haihuwa a Kasar Turkiyya

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yanka kek ɗin murnar ranar haihuwarsa a Turkiyya bayan ya cika shekara 79 da haihuwa.

An tsara kek ɗin da launin Najeriya wato fari da tsanwa inda bayan ya yanka kek ɗin sai ya tattauna da hadimansa kafin suka tafi wajen taron tattaunawa kan cinikayya tsakanin Turkiyya da ƙasashen Afrika.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa zai ci gaba da yin iya bakin ƙoƙarinsa wajen yi wa ƴan Najeriya aiki har zuwa lokacin da zai miƙa mulki a 2023.

Shugaban ya kuma ce zai koma gona ne domin ci gaba noma da kiwo bayan ya miƙa mulki.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...