Wasu matasa sun ƙone wani ɓangare na ofishin sanata Barau Jibrin a Kano, jigo a ɓangaren APC da ya raba gari da ɓangaren gwamnan jihar.
Shaidu sun bayyanawa BBC cewar matasan sun fi 100 da suka abka wa ofishin jam’iyyar.
Wannan na zuwa a yayin da wata kotu a Abuja ta rushe shugabancin ɓangaren gwamna Ganduje tare da tabbatar da jagorancin ɓangaren Shekarau.
Rikicin siyasar APC a Kano na ci gaba da ɗaukar hankali a Najeriya tun bayan gudanar da zaɓen shugabannin jam’iyyar ɓangare biyu, inda wasu ke ganin rabuwar kai a Kano wata babbar ɓaraka ce ga APC.
Sai dai Rahotannin da Kadaura24 ta samu sun nuna Cewa tuni Jami’an Rundunar Yan Sanda Suka Isa wajen domin hana karya doka da Oda.