An ritsa ƴan bindiga a gidan gyaran hali na Jos bayan da su kai yunƙurin ɓalle shi

Date:

 

Ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari gidan gyaran hali da ke Jos, Jihar Filato.

Francis Enobore, kakakin gidan gyaran halin ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi.

Ya ce ƴan bindigan sun dira a ƙofar shiga gidan gyaran halin ne da misalin ƙarfe 5:20 na yamma, inda su ka nufi babbar ƙofar shiga.

Su na dosar ƙofar, in ji Enobore, sai su ka buɗewa ma’aikatan gurin wuta, su ma kuma su ka maida martani, inda a hakan ne ƴan bindigar su ka samu damar ɓalle ƙofar su ka shiga harabar gidan.

Bayan sun samu shiga cikin gidan, ai kuwa sai a ka ritsa su bayan da a ka gaiyato sauran jami’an tsaro su ka yi wa gidan gyaran halin ƙawanya, in ji Enobore.

Daily Nigeria ta rawaito Enobore ya ƙara da cewa an kuma ƙaro dakaru da ga shalkwatar gidajen gyaran hali.

Ya ƙara da cewa yanzu dai an shawo kan lamarin, bayan da gamaiyar jami’an tsaro da a ka girke a wajen su ka mamaye gidan gyaran halin kuma sun fi ƙarfin ƴan bindigan.

Yayin da ƴan bindigar su ka shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi, Enobore ya sanar da cewa za a ci gaba da bada bayanai da zarar an wasu wani ci gaba a bisa lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...

Dalilan Hukumar tace fina-finai ta Kano na haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma’aiki S A W

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta...

‎Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano

‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu...