FAAN ta dakatar da wasu ma’aikata bisa zargin karɓar na-goro a hannun matafiyi

Date:

 

Hukumar kula da Filayen Jirgin Sama ta Ƙasa, FAAN ta sanar da dakatar da wasu ma’aikatanta bisa zargin karɓar na-goro a hannun wani matafiyi a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Jihar Legas.

Janar-Manaja mai kula da sashin Hulɗa da Jama’a, Henrietta Yakubu ce ta baiyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a yau Asabar a Legas.

Ta baiyana cewa wannan matakin dakatarwar da a ka ɗauka wani yunƙuri ne na kakkaɓe ɓata-garin ma’aikata da cin hanci a filin jirgin saman na ƙasa.

Yakubu ta ce ma’aikatan da abin ya shafa sun haɗa da na ɓangaren tsaron filin jirgin sama, AVSEC da kuma na ɓangaren kula da kwastomomi, inda ta ƙara da cewa dukkansu an dakatar da su.

Daily Nigeria ta rawaito Janar-Manaja ɗin ta ƙara da cewa an ɗauki matakin ne domin ya zama darasi ga sauran ɓata-gari na hukumar, waɗanda ba su da wani aiki sai na zubar da mutuncinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda kamfanin ganyen shayi na Z&Y ke fuskantar matsin lamba daga TOP TEAA

Wani matashin ɗan kasuwa daga jihar Kano, mai suna...

Gwamnatin Kano ta bayyana sunayen unguwannin da aka sami gurbatacciyar Iska

    Wani rahoto na mako-mako kan yanayin lafiyar iska da...

Sallah: Gwamnatin Kano za ta hukunta gidan wasan da ya bar masu shigar banza da shaye-shaye

Daga Rahama Umar Kwaru   A kokarin ta na yaki da...

Sallah: Hussari ya sauke kabakin arziki ga yan jam’iyyar APC na karamar hukumar Gwale

Daga Ibrahim Abubakar Diso   Tsohon Dan Majalisar wakilai da ya...