FAAN ta dakatar da wasu ma’aikata bisa zargin karɓar na-goro a hannun matafiyi

Date:

 

Hukumar kula da Filayen Jirgin Sama ta Ƙasa, FAAN ta sanar da dakatar da wasu ma’aikatanta bisa zargin karɓar na-goro a hannun wani matafiyi a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Jihar Legas.

Janar-Manaja mai kula da sashin Hulɗa da Jama’a, Henrietta Yakubu ce ta baiyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a yau Asabar a Legas.

Ta baiyana cewa wannan matakin dakatarwar da a ka ɗauka wani yunƙuri ne na kakkaɓe ɓata-garin ma’aikata da cin hanci a filin jirgin saman na ƙasa.

Yakubu ta ce ma’aikatan da abin ya shafa sun haɗa da na ɓangaren tsaron filin jirgin sama, AVSEC da kuma na ɓangaren kula da kwastomomi, inda ta ƙara da cewa dukkansu an dakatar da su.

Daily Nigeria ta rawaito Janar-Manaja ɗin ta ƙara da cewa an ɗauki matakin ne domin ya zama darasi ga sauran ɓata-gari na hukumar, waɗanda ba su da wani aiki sai na zubar da mutuncinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...