Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano ta ce ta cafke wani fitinannen ɗan damfara, wanda ya damfari mutane da dama ta kafar sadarwa.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abdullahi Kiyawa ya fitar a jiya Litinin, mutumin mai suna Aliyu Hussaini ɗan unguwar Hotoro mai shekara 25, ya ƙware wajen sanya hotunan atamfofi, shaddoji, lesuna da sauransu ta kafar facebook ko WhatsApp.
Kiyawa ya ce idan ya saka hotunan, sai mutane su riƙa nuna buƙatar su, sai su daidaita da shi, su aiko masa da kuɗin kayan amma kuma sai ya yi ƙememe ya ƙi aika musu da kayan.
Kakakin ya ƙara da cewa dubun ɗan damfarar ta cika ne bayan da wata mata daga Yelwa Shandam ta Jihar Filato ta kawo ƙararsa shalkwatar ƴan sandan ta Kano, inda ta yi ƙorafin cewa wani mutum a facebook mai suna Aliyu Hussaini Salisu ya sanya hotunan lesuna da shaddoji ita kuma ta zaɓi kala 14 daga ciki.
Matar ta ƙara da cewa kuɗin kayan da ta zaɓa ya kama naira dubu 100, inda ya ce ta aiko masa ta tashar mota ta unguwa uku, shima kuma zai aika mata da kayan ta nan.
Bayan ta aiko masa da naira ɗari cif-cif, mai makon Hussaini ya aika mata da kayan da ta zaɓa, kawai sai ya naɗe tsimmokara har da tsohon gidan sauro a cikin leda, ya manne da salatif ya aika mata.
Daily Nigeria ta rawaito Kiyawa ya ƙara da cewa, da jin wannan ƙorafi na matar, sai Kwamishinan Ƴan Sanda, Sama’ila Shu’aibu Dikko ya umarci dakarun binciken sirri, ƙarƙashin jagorancin DSP Muntari Jibrin Dawanau domin cafko mai laifin.
Ai kuwa ba da daɗewa ba, sai waɗannan dakaru su ka samu nasarar damƙe ɗan damfarar nan a tashar mota ta unguwa uku, inda a ka samu na’urar laftof da waya a tare da shi.
Da dumi-dumi : Yan Sanda sun ceto Ma’aikatan Jami’ar Abuja da aka sace
Kiyawa ya baiyana cewa, a yayin titsiye da a ka yi masa, Hussaini ya amsa laifinsa inda ya ce idan ya karɓe kuɗaɗen mutane, sai ya toshe su ta facebook da WhatsApp ɗin.
Kiyawa ya ƙara da cewa bayan an kama mai laifin, sai ga mutane har 37 sun yi tururuwa sun kawo ƙorafe-ƙorafe a kan sa da cewa ya damfare su har sama da naira miliyan ɗaya.
DPO ya lashe musabaƙar Alƙur’ani ta ‘yan sandan Kano
Kakakin ya baiyana cewa a jiya Litinin a ka kai mai kaifin babbar kotun majistire da ke Ungoggo domin ya girbe abin da ya shuka.