Zamu dawo da Martabar Arewan Nigeria duk da Kalubalen da Zamu fuskanta – Gidado Mukhtar

Date:

Daga Rukayya Muhd Kabara

 

Shugaban kwamitin Am8ntattu na Kungiyar farfado da martabar arewa Wato Northern Reform Organization Alhaji Gidado Mukhtar yace har Yanzu ba’a makaraba za’a iya dawo da martabar arewacin Kasar nan Kamar yadda yake a baya.

Alhaji Gidado Mukhtar ya bayyana hakanne Yayin taron wayar da Kai da Kungiyar su ta Shirya domin zaburar da Yan arewa su tashin din dawo da martabar Yankin.

Yace an tafka kura-kura Masu tarin yawa a baya Waɗanda sune ummul aba’isin Matsalolin Rashi tsaro da Rashi Ilimi da Kuma Rashin hadin Kai da a Yanzu ake fama dasu a arewa , Waɗanda Kuma su Suka Hana arewan cigaba.

Alhaji Gidado Mukhtar yace sun Samar da Kungiyar farfado da martabar arewan ne domin Magance Wadancan Matsaloli tare da ciyar da arewan gaba, ta dawo da kimarta Kamar yadda take Lokacin su Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.

Game da sauya fasalin Kasar nan, Alhaji Gidado Mukhtar yace basa goyon Bayan sauya fasalin Saboda Masu kiraye-kirayen basu da Wata hujja da za’a gamsu da ita har a sauya fasalin Kasar.

Farfesa Abdullah Uba Adamu na Jami’ar Bayero dake nan Kano Yana daga Cikin Malaman da Suka gabatar da makala yayen taron yace ya Zama wajibi manyan kabilun Arewacin Ƙasar nan su Rika dauka Suma Kananan kabilu da suke Yankin Suna Suna da Gudummawa da zasu bayar wajen farfado da martabar arewan.

Yaca ba dai-dai bane manyan kabilu su Rika ganin su Kadai zasu iya kawowa arewa sauyi Saboda Sauran kabilun suma Suna da hakkin a saka su Cikin duk Wata sabga data safin arewan tunda Allah ne yayi a Yankin.

Taron Wanda aka gudanar da shi a Gidan mumbayya dake nan Kano ya Sami halartar al’umma daban-daban daga Arewacin Nigeria.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...