Shirin Bunkasa Noma da Kiwo zai daga Darajar Wasu Kasuwanni Shanu a Kano

Date:

Daga Abdulrasheed B Imam
 Shirin bunkasa noma da makiwo na jihar Kano, KSADP, zai gyara tare da inganta kasuwar shanu ta Falgore dake karamar hukumar Doguwa da wasu irin kasuwanni guda hudu a fadin jihar.
 Ayyukan da za’a gudanar a kasuwannin sun hada da samar da wajen lodin kaya, wuraren shayar da babbobi ruwa, magudanun ruwa, ofisoshin yada labaran, tsaro, da ofishin Jami’an kula da kiwon lafiyar dabbobi, fitulun tare Kuma da gina ban daki.
 Jami’in kula da Shirin na jiha, Malam Ibrahim Garba Muhammad ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin wakilan kungiyoyin Manoma da Makiyaya mazauna dajin Falgore, wadanda suka ziyarce shi a ofishin aikin.
 Cikin Wata sanarwa da Jami’in yada labaran Shirin Ameen Yassar ya aikowa Kadaura24 yace Shugaban Shirin ya kara da cewa shirye-shirye sun yi nisa wajen samar da a kalla cibiyoyin tattara madara guda biyar a yankin Falgore, “ta yadda mutanen ku za su iya karbar madarar a wuri daya, su Kuma kaita kasuwa, Kun ga Idan hakan ta tabbata matanku sun daina shan wahalar tafiya birni don sayar da madara”.
 Malam Ibrahim ya bukaci al’ummar dajin na falgore da su baiwa Shirin bunkasa noma da kiwo goyon baya domin cimma manufofinsa, yana mai jaddada cewa da yawa daga cikin ayyukan da aka yi za su kawo canji ga rayuwar makiyaya.
 Tun da farko wakilan kungiyoyin Makiyaya da Manoman, Malam Haruna Mu’azu da Ardo Umar Lawan Motar Kara sun bukaci Shirin ya samar wa ‘ya’yansu makarantu, Sannan a saka ‘ya’yansu Cikin duk Wani Aiki da za’a yi musu a yankunan.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kudin 2026 da ya kai N1.368 tiriliyan

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar...

Nazarin Yadda Shaharar Sanata Barau Ta Karade Nigeria – Abba Anwar

Daga Abba Anwar Wani babban abin lura game da rayuwar...

Kungiyar Ɗaliban Mariri ta gudanar da aikin duba marasa Lafiya kyauta a yankin

Daga Abdallahi Shu'aibu Hayewa   Kungiyar Dalibai ta Makarantar Mariri wato...

Gwamnan Taraba ya bayyana dalilinsa na shirin komawa APC

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai shiga...