Kalaman Ɓatanci: Shekarau ya shirya bita ga ƴan Social Media

Date:

Daga Khalifa Abdullahi Maikano

 

Sanatan kano ta tsakiya Malam Ibrahim shekarau ya shirya taron bita ga ƴan social media na gidan sa domin faɗar da su yadda zasu rika tallata sanatan da kuma yadda zasu gujewa yada labaran ƙarya .

Yayin taron sanata Shekarau ya bukaci mahalatta taron da su guji ya da labaran karya koda akan yan hammayya ne ,domin yin karya yana zubar da kimar dan adam.

” ku guji yin kalaman ɓatanci akan kowa saboda duk abun da kayi kai ma za’a yi maka , idan ka ɓata gwani wani, shi wanda ka ɓata gwaninsa shi ma zai ɓata naka gwani ka ga kenan an yi ba’ai ba.” Inji Sanata Shekarau

Sanatan yace kusan shekara guda kenan yana son shirya irin wannan bitar saboda yan social media su dai na yada labaran karya dana ɓatanci domin dai-daita al’amuran.

“Nasan wasun ku zasu yi tunanin an shirya wannan taron ne domin abun da yake faruwa a cikin jam’iyyar mu, to ina so ku wannan taron bashi da alaƙa da wannan matsalar waccan daban wannan daban kuma idan lokacin waccan yayi zamu magana akai.” inj Shekarau

An dai gayyato masana da dama wajen taron domin fadakar da mahalarta taron cikin su har da Daraktan yada labaran sanatan Malam Sule Ya’u Sule.

8 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano Ta Karyata Rahoton Cibiyar Wale Soyinka Kan Take ‘Yancin ‘Yan Jarida

Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da rahoton da...

Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Cire Maryam Sanda Daga Jerin Wadanda Za a Yi Wa Afuwa

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bada umarnin a...

Majalisar Kano ta buƙaci a soke ɗaukar aikin kwastam da aka yi a kwanan nan

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira ga dukkan...

‎ ‎Kuskure ne Tinubu ya cigaba da ciyo wa Nigeria bashi bayan ya cire tallafin mai – Sarki Sanusi

‎ ‎ ‎Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN),...