Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya Inec ta ce an samu matsaloli da suka kawo cikas ga harkokin zaɓen gwamnan jihar Anambra.
Hukumar ta kuma amince da cewa wasu na’urorin tantance masu zaɓe sun samu matsala yayin da ta kasa tura jami’anta a wasu wuraren, kamar yadda shugaban hukumar a Anambra Nkwachukwu Orji ya shaida wa manema labarai.
Ya ce hukumar za ta yi amfani da dokoki da tsarinta na karɓar sakamakon zaɓe.
BBC Hausa ta rawaito Shugaban hukumar ya ce inda aka samu matsala za a iya tattara sakamakon a cibiyoyin tattara sakamako na ƙananan hukumomi.