Dr. Gawuna ya dora Alhakin Magance Rikicin Manoma da makiyaya ga Masu Ruwa da tsaki a Kasar nan

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa

Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma kwamishinan harkokin noma, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya bukaci masu ruwa da tsaki a kasar nan da su lalubo hanyoyin da za’a yi amfani da su a cikin gida wadanda za su magance matsalolin da ke haddasa rigingimun manoma da makiyaya a sassan kasar nan.

Ya kuma jaddada cewa, shiga tsakanin irin wadannan rikice-rikicen a kan lokaci da shugabannin gargajiya ke yi shi ne dabarun hana tabarbarewar doka da oda, ta yadda za a ceto rayuka da dukiyoyin halaka.

Mataimakin Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani sakon da ya aikewa wajen bikin bude horo na kwanaki 5 kan yadda za a shawo kan rikice-rikice da kuma warware rigingimun da aka yi, ga kwamitin fitar da burtalai na jihar Kano wanda kungiyar raya manoma ta jihar Kano, KSADP, da Kamfanin SMAKAIYA Agricultural Consult Limited suka shirya a The Afficent. a cikin birnin Kano.

Cikin Wata sanarwa da Jami’in yada labaran Shirin bunkasa noma da kiwo na Jihar Kano ya aikowa Kadaura24 yace Dr. Gawuna wanda ya samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar noma, Malam Balarabe Hassan Karaye, ya ce: “Wannan batu na rikicin manoma da makiyaya abu ne mai matukar barazana ga tsaron kasa wanda ya kamata a yi taka-tsantsan akan sa. Maganin rikice-rikice da ake samu ya zama dole don Samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, wanda in ba haka ba gwamnati ba za ta iya aiwatar da ayyukan ci gaba ba”.

Dr. Gawuna ya nuna godiya ga Bankin Raya Musulunci, Asusun bunkasa Rayuwa al’umma da kuma Asusun Hadin Kai na Musulunci, bisa tallafin da suke bayarwa wajen cimma manufar aikin.

A nasa jawabin, Manajan Daraktan KNARDA, Dokta Junaidu Yakubu Muhammad, ya ce gwamnatin jihar ta kafa kwamitin Masu ruwa da tsaki a matakin jiha da kananan hukumomi, domin dakile rikicin da ya shafi makiyaya da manoma.

“Ta hanyar shirin bunkasa noma da kiwo na jihar Kano, gwamnatin jihar ta nuna kudirinta don zamanantar da noma da kiwo.”

Jami’in kula da ayyukan noma na jihar Kano, Malam Ibrahim Garba Muhammad, ya bayyana cewa magance rikice-rikicen na da matukar muhimmanci wajen cimma burin ci gaban aikin gona gaba daya, yana mai jaddada cewa “babu wanda zai iya zuwa gona ko kiwon shanu ko sayar da nono idan babu zaman lafiya”.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...