Zaben APC: Bamu Sami korafi ko daya ba a Kano – Kwamitin APC

Date:

Daga Sani Danbala

 

Kwamitin karbar korafe-korafen zaben Shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar anan kano yace yazuwa Wannan Lokaci babu Wani korafi da Suka karba Dangane da zaben da aka gudanar a filin Wasa na Sani Abacha dake Kofar mata.

Shugaban Kwamitin Dr Tony Macfoy ne ya bayyana hakan Yayin Wata ganawa da sukai da Manema labarai a helkwatar jam’iyyar APC ta Jihar Kano.
Dr. Macfoy Wanda daka Kwamitin yace Rashin Samun korafi akan wancan zaben daga ko Mutum daya ya nuna cewa kowa ya Amince da yadda aka gudanar da zaben .
” mun yi Zama na kusan kwanaki uku, Amma har yanzu Babu ko Mutum daya daya Zo domin Mika Rahoton korafinsa”.
Sai dai Shugaban Karamar yace zasu je hutun Rabin Lokaci ,Inda zasu fara rubuta Rahotonsu domin mikawa ga uwar jam’iyyar APC ta Kasa dake Abuja .
“Muna nan kano har Ranar asabar Mai zuwa ,Kuma duk Wanda Zai Kawo korafi game da zaben a Shirye Muke mu karba Kamar yadda kundin tsarin Mulkin jam’iyyar APC ya tanada”.
Kwamitin Mai Mutane 5 ya Fara Zaman karbar korafe-korafen ne tun Ranar asabar din data gabata a helkwatar jam’iyyar APC ta kano dake kan titin maiduguri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...

Dalilan Hukumar tace fina-finai ta Kano na haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma’aiki S A W

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta...

‎Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano

‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu...