Daga Nura Abubakar
Mataimakin gwamnan jihar Kano Dr.Nasiru Yusuf Gawuna ya yi kira da a zauna tare a zauna lafiya tsakanin al’ummar kasar nan.
Ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadin nan a Abeokuta, Jihar Ogun yayin bikin mauludi na Karo na 55 da Kungiyar Musulunci ta Attoreeqatul Qadiriyya Al-Azeeziyah ta shirya don murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam).
Ya yi kira da a zauna lafiya, tare da nuna kauna, hakuri da Sauran kyawawan dabi’u ga al’umma domin haka addinan Musulunci ya koyar.
Cikin Wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran Mataimakin Gwamnan Hassan Musa Fagge ya aikowa Kadaura24 yace Dr. Gawuna ya roki Musulmai da su sanya hadin kai, kauna, hakuri da juriya a harkokin su na yau da kullum kamar yadda Annabi Muhammadu ya koyar.
“Ina farin cikin kasancewa a nan don murnar haihuwar, Wanda yafi kowa a wajen Allah wato masoyinmu Annabi Muhammad (SAW)”.inji Gawuna
“Lokacin da Khalifan Qadiriyya ya gaya mani cewa yana gayyata ta zuwa wannan taron, nan da nan na sanar da shugabana Gwamna Ganduje wanda ya ce shi da Kan sa Zai so ya kasance a wannan taron mai albarka”.
Ya bukaci musulmi da su ci gaba da yin koyi da koyarwar Annabi Muhammadu tare da yin kira gare su da su kasance masu kiyaye hakkoki junan su.
Bayan yayi Kira ga al’umma dasu dage da addu’o’in Samun Zaman lafiya da cigaban kasa, Gawuna ya ba da gudummawar Naira miliyan 2 a matsayin tallafi ga wadanda suka shirya taron mauludin.
Da yake magana da Khalifa na Harkar Qadiriyya a Afirka, Sheikh Qariballah Nasiru Kabara ya bayyana cewa makasudin taron shi ne nuna soyayya da yin tuni kan halayen Annabi Muhammad (SAW).
Ya yi nuni da cewa son Annabi Muhammad S A W zai kai Musulmi ga Samun Jannatul Firdaus.
Ya nuna godiya ga Mataimakin Gwamnan Kano saboda halartar bikin mauludi.
Tun da farko a nasa jawabin Aare Qadiriyya na Najeriya, Alh.Najimdeen Jumah ya ce alakar da ke tsakanin Kano da Abeokuta ta samo asali ne tun da dadewa ta hannun mutane irin su Marigayi Sheikh Nasiru Kabara wanda ya ba da gudummawa mai yawa ci gaban addinin Musulunci kuma ya bar abubuwan da suka wanzu kamar taron mauludi da dai Sauransu.