Alh. Yahaya Datti ya Zama Shugaban rikon Kungiyar Masu Dankalin turawa ta kasa

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa
Kungiyar masu Sana,ar dankalin turawa ta kasa ta zabi Shugabaninta na riko Waɗanda zasu tafiyar da harkokin Kungiyar kafin Zabe.
Alh yahaya Adamu Datti shi aka nada a matsayin shugaban rikon Kungiyar,Wanda Kuma kafin Wannan lokaci shi ne Shugaban Kungiyar anan kano.
Da yake jawabi shugaban rikon yace a karkashin jagorancin nasa zaiyi iya bakin kokarinsa wajen ganin yakai kungiyar ga matakin da kowa zai yi Alfahari da ita .
Yace dama yasan Kalubalen da Kungiyar take fuskanta don Haka Zai hada Kai da Masu Ruwa da tsaki dama duk ‘ya’yan Kungiyar domin Magance Matsalolin da Kungiyar take fama da su.
Alhaji Yahya Datti ya Nemi hadin Kan ‘ya’yan Kungiyar domin inganta harkokin sana’ar su ta Sayar da dankalin turawa a duk fadin kasar nan.
Shugaban Karamar Hukumar Tarauni Alhaji Habu Zakari shi ne ya wakilci Gwamnan Kano a Wajen taron  yace gwamnatin Kano za tayi aiki kafada da kafada da  Shugabanin rikon kungiyar domin samun nasarar da aka sanya a gaba.
“Akwai namu a Cikin ku Wato Abdullahi Maikano Zara Wanda Mataimaki na Musamman ne ga Gwamnan Kano hakan ta nuna kuna yi da Gwamnatin Kano don haka Muna zamu yi daku ko dan Maikano Zara”. inji Habu P A
Shugaban Karamar Hukumar ta Tarauni yasa alwashin bada duk Wata Gudunmawar da Kungiyar take bukata daga Gwamnati domin ciyar da Kungiyar gaba.
Taron Wanda ya gudana a nan kano ya Sami halartar Masu sana’ar Dankalin turawa daga sassa daban-daban na Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...